DOWNLOAD HERE

News

Zamba: Kotu ta ba da belin abokin Yahaya Bello, Abdulsalami Hudu a kan N300m

DOWNLOAD HERE

Zamba: Kotu ta ba da belin abokin Yahaya Bello, Abdulsalami Hudu a kan N300m
Written by Areatatafo

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin Abdulsalami Hudu, wanda ake zargin tare da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan zargin zambar kudade a lokacin gwamnatinsu.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ce ta gurfanar da su a gaban kotu.

Make money online

Mai shari’a Maryam Anenih ta bayar da belin ne ranar Talata, tare da sharuɗɗa masu tsauri. An sanya belin a kan naira miliyan 300 (N300m).

Kotun ta bukaci Hudu, wanda shi ne wanda ake tuhuma na uku a shari’ar, da ya gabatar da masu tsaya masa guda biyu, kowanne da kadarar ƙasa da ke yankin kotun, musamman a Maitama.

Kadarar dole ta zama mai darajar da ba ta gaza N300m ba, kuma sai magatakardar kotun ya tabbatar da sahihancin takardun mallakar kadarar.

Haka kuma, an umarci Hudu da kada ya bar Najeriya ba tare da izinin kotu ba. Zai ci gaba da zama a cibiyar gyaran hali ta Kuje har sai ya cika sharuɗɗan belin.

An kuma bukaci wanda ake tuhuma da masu tsaya masa su gabatar da hotunan fasfo guda biyu da suka sabunta ga kotun.

Bugu da ƙari, Hudu ya kamata ya mika dukkanin takardun tafiyarsa ga kotu.


Leave a Comment

//nijairsauftoa.net/4/7617614