DOWNLOAD HERE

News

Za a kafa kotuna don warware rikicin fasinjojin jiragen sama

DOWNLOAD HERE

Za a kafa kotuna don warware rikicin fasinjojin jiragen sama
Written by Areatatafo

Hukumomi a bangaren sufurin jirgin sama sun kammala shirin kafa kotunan tafi da gidanka a filayen jirgin sama domin hukunta fasinjojin da kan tayar da tayar da fitina.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wasu fasinjoji kan yi zanga-zanga kan jinkiri ko soke tashin jirgi har su kai ga dukan ma’aikatan jirgin ko lalata kayan aiki a filayen jirgin.

Make money online

Hukumar filayen jiragen sama FAAN da takwararta ta sufurin jiragen sama NCAA sun nuna rashin jin dadinsu kan wannan hali, inda suka tsara wasu matakan magance matsalar, ciki har da tsawaita awannin aiki a filayen jirgin sama zuwa ƙarfe 10:00 na dare.

A wani taron masu ruwa da tsaki da NCAA ta shirya don tattaunawa kan matsalolin da ke haddasa jinkirin taahin jirage, an cimma matsaya cewa filayen jirgin sama da ke da kayan aiki za su yi aiki har zuwa ƙarfe 10:00 na dare.

Taron, wanda ya gudana a ofishin NCAA a Legas, ya samu halartar shugabar FAAN, Mrs. Olubunmi Kuku, wakilan NAMA, NIMET, da kuma shugabannin kamfanonin jiragen sama karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban AON, Mr. Allen Onyema.


Leave a Comment

//rausteehih.net/4/7617614