Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya ce binciken EFCC ya tabbatar da rukunin gidajen da aka mayarwa gwamnati, mallakin tsohon gwamnan bankin CBN ne.
Ya ce jaridarsa ta Empowered Newswire ta samu tabbacin cewa Godwin Emefiele ne ya mallaki gidaje 753 da sauran gine-gine da aka mayarwa gwamnati a Abuja.
Laolu Akande ya ce sun samu takardun kotu da su ka nuna yadda Mr. Emefiele da wadans mutane su ka mallaki gidajen ta barauniyar hanya.
Tsohon mai Magana da yawun Yemi Osinbajo ya yaba da yadda EFCC ta yi kokarin kama Mr. Godwin Emefiele da sauran mutanen da ake zargi a badakalar.
Amma bayanin Laolu Akande ya jawo masa mutane sun soki gwamnatin baya, tare da zargin cewa a karkashin ikonsu aka yi satar.
@royaltyuso ya ce ba lallai Laolu Akande ya iya furta kalaman ba da kafin shekarar 2023.
@procyvir ya tambayi Laolu Akande ko yaushe za a kai Godwin Emefiele a domin a harbe shi.
Godwin Emefiele shi ne gwamnan babb bankin Najeriya a lokaci da gwamnatin Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo