DOWNLOAD HERE

News

Wani Jirgin yakin Najeriya ya sake kuskuren kai hari kan wasu kauyuka a Sokoto

DOWNLOAD HERE

Wani Jirgin yakin Najeriya ya sake kuskuren kai hari kan wasu kauyuka a Sokoto
Written by Areatatafo

Jirgin yakin da zai kaiwa Lakurawa hari ya kauce hanya ya kashe mutane da dama a jihar Sokoto.

An zargi cewa mutane da dama sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani farmakin jirgin yaki da ya yi kuskuren jefa bama-bamai kan wasu al’ummomi biyu a karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

Make money online

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe bakwai na safe a ranar Laraba, inda jirgin yakin da aka tura don kai hari kan sansanin ‘yan ta’addan Lakurawa ya jefa bama-bamai a kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa.

Wani mazaunin yankin, Malam Yahya, ya ce kauyukan biyu suna kusa da dajin Surame wanda ake gannin ya zama mafakar ‘yan ta’addan Lakurawa da ‘yan bindiga.

Wata majiya ta bayyana cewa fiye da mutane goma ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a harin.

Shugaban karamar hukumar Silame, Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa suna ci gaba da tantance barnar fa aka yi.


Leave a Comment

//wousuzebostu.net/4/7617614