Memba na Majalisar Wakilai daga mazabar Yagba, Hon Leke Abejide, a ranar Laraba ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda zai canza Najeriya.
Abejide, wanda ya kasance bako a shirin Politics Today na Channels Television, ya nuna kwarin gwiwa da mulkin Tinubu wajen daidaita al’amuran kasar.
“Idan muka kai shekara ta 2026, za mu ga wannan kasa yadda zai koma, kowa zai yaba wa Tinubu. Ina fadin shine ceton da Najeriya ke bukata yanzu kuma zai iya gyara Najeriya,” in ji dan majalisar.
Abejide, mamba daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya kara da cewa Tinubu zai fitar da kasa daga cikin mawuyacin hali.
Dan majalisar ya soki mulkin Muhammadu Buhari kan yadda aka sarrafa tattalin arzikin kasa a lokacin sa.