DOWNLOAD HERE

News

Tinubu da Shettima zasu kashe biliyan 9.36 a tafiye-tafiye da makulashe a kasafin 2025

DOWNLOAD HERE

Tinubu da Shettima zasu kashe biliyan 9.36 a tafiye-tafiye da makulashe a kasafin 2025
Written by Areatatafo

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima za su kashe Naira biliyan 9.36 kan tafiye-tafiye na cikin gida da waje, tare da kayan sha da abinci a shekarar 2025.

Wannan na kunshe cikin kudurin kasafin kudin shekarar 2025 da shugaban kasa ya gabatar na tiriliyan 49.7 ga majalisar hadin gwiwar zaman majalisar tarayya.

Make money online

A cewar kasafin kudin, Tinubu zai kashe Naira biliyan 7.44 kan tafiye-tafiye da kayan ciye-ciye, yayin da Shettima zai kashe Naira biliyan 1.9.

Tafiye-tafiyen shugaban kasa zuwa kasashen waje a shekarar 2025 za su ci Naira biliyan 6.14, yayin da na cikin gida za su ci Naira miliyan 873.9.

Haka zalika, an ware Naira miliyan 431.6 domin kayan sha da abinci, da kayan girki na shugaban kasa. Mataimakin shugaban kasa zai kashe Naira biliyan 1.31 kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a 2025, yayin da na cikin gida za su ci Naira miliyan 417.5.

Kayan sha da abinci da kuma kayan girki na mataimakin shugaban kasa za su ci Naira miliyan 186.02.

A shekarar 2024, Shugaba Tinubu, Mataimaki Shettima, da uwargidansa Remi Tinubu, sun kashe akalla Naira biliyan 5.24 kan tafiye-tafiye na cikin gida da waje daga watan Janairu zuwa Maris, a cewar wani bincike kan kudaden tafiyar da aka yi amfani da shi a shafin GovSpend, wani dandalin fasaha da ke bin diddigin kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa.


Leave a Comment

//couledochemy.net/4/7617614