Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Lagos domin gudanar da bukukuwan kirsimeti da Sabuwar shekara.
Shugaban ya sauka a sashen musamman na filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Lagos da misalin karfe 3:23 na rana, a ranar Laraba, 18 ga Disamba.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Da isarsa Lagos, gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos tare da mataimakinsa, Dr. Femi Hamzat; mambobin majalisar zartarwa ta jihar Lagos; da shugabanni na jam’iyyar APC mai mulki a Lagos sun tarbi shugaban kasa a filin jirgin saman.
Kafin tafiyarsa daga Abuja, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasa don nazari da amincewa.