DOWNLOAD HERE

News

NNPC ya kaddamar da jarabawar CBT ga masu neman aiki

DOWNLOAD HERE

NNPC ya kaddamar da jarabawar CBT ga masu neman aiki
Written by Areatatafo

Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC ya bayyana sabbin bayanai dangane da shirin daukar ma’aikata da ake gudanarwa.

A ranar Asabar ne Kamfanin NNPC ya fara gudanar da jarabawar kwamfuta, CBT domin tantance masu neman aiki a wasu mukamai daban-daban a kamfanin.

Make money online

Wannan mataki na daya daga cikin matakan daukar ma’aikata da kamfanin ke aiwatarwa don cike guraben aiki a bangarori daban-daban.

NNPCL ya bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Asabar, inda ta nuna cewa mutane 45,689 ne ke neman guraben aikin da ake da su.

NNPCL ya bayyana cewa kawai wadanda suka fi cancanta za su samu damar cin gajiyar shirin daukar aikin da ake gudanarwa.

Shugaban Kamfanin NNPCL, Mele Kyari, wanda ya kai ziyara zuwa daya daga cikin cibiyoyin jarabawar, ya tabbatar da cewa za a gudanar da tsarin ne cikin sauki, gaskiya, adalci, da kuma sahihanci.

“A matsayin kamfani mai bayar da dama ga kowa, NNPC Ltd. ta tanadi wasu abubuwan musamman don tabbatar da cewa masu neman aikin da ke da nakasa za su iya shiga jarabawar ba tare da wata tangarda ba,” in ji Kyari.

A tunatarwa, a watan Yuli na shekarar 2024, mai magana da yawun NNPCL ya sanar da fara sabon shirin daukar ma’aikata.


Leave a Comment

//auwhothaishob.net/4/7617614