DOWNLOAD HERE

News

Musulunci bai hana mata karatu ba – Sarkin Musulmi

DOWNLOAD HERE

Musulunci bai hana mata karatu ba – Sarkin Musulmi
Written by Areatatafo

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar lll, ya ce musulunci ba ya hana yara mata karatu.

Sarkin ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a Bauchi wajen taron shirin inganta ilimin mata na AGILE, wanda ma’aikatar ilimi ta jihar Bauchi ta haɗa tare da babban bankin duniya.

Make money online

Taron mai taken: “kawo ƙarshen abubuwan da suke hana mata zuwa makaranta a arewa maso gabas: Rawar da sarakunan gargajiya da malaman addini za su taka.”

Sarkin Musulmin ya ce, “Musulunci ba ya hana yara mata neman ilimi. Akwai wasu abubuwan da suke kawo musu tsaiko wajen neman ilimi.

Yace a hanyar sa ta zuwa wajen wannan taro ya ga ƙananan yara suna talla a titi. Inda daya tambaye su, sai suka ce akwai makarantar safe da ta yamma.

Sarkin yace tabbas karatun yara mata na da muhimmanci saboda su ne za su ilimantar da iyalinsu da al’umma.

Ya yi kira ga gwamnonin arewa su ƙara zuba kuɗaɗe a ɓangaren ilimi domin ilimantar da yaran yankin baki daya.


Leave a Comment

//juchacmibouche.net/4/7617614