Wani mummunan hadarin motar a hanyar Maiduguri da ya rutsa da ma’aikatan jami’ar jihar Borno ya yi sanadin rasa rayukan mutane uku, yayin da 30 jikkata.
Hadarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da wata babbar motar daukar kaya ta fada cikin gefen motar jami’ar.
An kai wadanda suka samu raunuka kai tsaye zuwa Asibitin Kwararru na Umaru Shehu, inda ake ba su kulawar gaggawa.
Ana ci gaba da kokarin samar da kulawa ga wadanda suka ji rauni yayin da aka dauke gawarwakin wadanda suka rasu don a yi musu jana’iza.