Majalsar dattawan Najeriya ta dakatar da tattauna kudurin dokar harajin da gwamnati ta aika mata, wanda ya jawo cece-kuce.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ne ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba.
Sanata Barau ya ce an umarci kwamitin kudi na majalisar ya dakatar da aikin da yake yi har sai wani kwamiti na musamman ya zauna da babban lauyan Najeriya.
Umarnin majalisar na zuwa ne bayan shugaban kasa ya umarci ma’aikatar shari’a ta yi aiki da majalisa wajen sake duba kudurin dokar.
Sanata Barau Jibrin na daga cikin yan majalisa da su ka fuskanci kalubale da martani daga mutane saboda nuna goyon bayan kudurin dokar harajin.