Jam’iyyar Labour Party ta sha alwashin daukar matakin shari’a kan mambobinta guda hudu na majalisar wakilai da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Mambobin da suka sauya shekar sun hada da Chinedu Okere, Mathew Donatus, Akiba Bassey, da Esosa Iyawe.
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya sanar da sauyin shekar a ranar Alhamis, yana mai cewa “rikicin cikin gida” a cikin LP ne ya sa suka sauya sheka.
Sai dai kakakin jam’iyyar LP, Obiora Ifoh, ya bayyana cewa babu wanda ke da ikon sauya sheka da kujerar jama’a
A cikin wata sanarwa, Ifoh ya ce: “Ko da yake shugabancin LP bai karaya ba kan wannan sauyin shekar, ya zabi kada ya bar abin ya wuce haka, kuma saboda haka ya umarci tawagar lauyoyinsa da su fara daukar matakin shari’a kan wadanda suka sauya shekar da kuma fara aiwatar da dawowa da kujerarmu bisa tanadin kundin tsarin mulki na 1999 da dokar zabe ta 2022 da aka yi wa gyara.
“Akwai cikakken zaman lafiya a LP, don haka, babu wanda aka zayɓa a karkashin tutar LP da ke da kariyar doka don ficewa daga jam’iyyar tare da mukamin jam’iyyar.”