DOWNLOAD HERE

News

Kwararrun likitoci na son a kara shekarun ritaya zuwa 70

DOWNLOAD HERE

Kwararrun likitoci na son a kara shekarun ritaya zuwa 70
Written by Areatatafo

Kungiyar likitoci ta kasa (MDCAN) ta bayyana cewa Ministan Lafiya Farfesa Muhammad Pate, zai gabatar da takarda ga Majalisar Zartaswar Tarayya kan bukatunsu na daidaita shekarun ritayar kwararrun likitoci zuwa shekaru 70.

Haka kuma, Pate tare da Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, sun shirya gabatar da takardar hadin gwiwa ga Kwamitin Shugaban Kasa kan Albashi, suna goyon bayan aiwatar da tsarin albashin da aka tsara (CONMESS) ga dukkan malaman likitanci.

Make money online

Kungiyar ta shiga yajin aiki na gargadi na tsawon kwanaki bakwai tun daga ranar 18 ga Nuwamba, don nuna muhimmancin wadannan bukatunsu. Sai dai, an dakatar da yajin aikin bayan kwanaki shida, bayan da gwamnati ta shigo cikin rikicin da ya shafi mukamin Mataimakin Shugaban Jami’ar Nnamdi Azikiwe wanda aka warware.

Kungiyar ta sake jaddada bukatarta na daidaita shekarun ritayar kwararrun likitoci zuwa shekaru 70 da kuma aiwatar da tsarin albashin CONMESS ga dukkan likitoci da hakora.

Da yake magana da wakilinmu a ranar Talata, Shugaban MDCAN, Farfesa Muhammad Muhammad, ya tabbatar da ci gaba kan takardun.

“Muna da masaniya kan daftarin takardar kuma mun bayar da shawarwarinmu, amma ban san matsayin da takardar take a yanzu wajen ministocin ba. Suna kan hanyar gabatar da ita ga Majalisar Zartaswa don tantancewa,”inji shi.


Leave a Comment

//psoahegauku.net/4/7617614