Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP ya yi kira ga shugabanni daga yankin Arewa ta Tsakiya su fitar da wanda zai maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Iyiorchia Ayu.
Dr. Ayu ya sauka daga mukaminsa kafin cikar wa’adinsa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP.
Wannan shawara ta fitota cikin sanarwa da aka fitar bayan taron gaggawa da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar PDP a Abuja ranar Alhamis, karkashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara.
Kwamitin ya kuma gargadi kwamitin gudanarwa na kasa (NWS) wajen samun jinkiri wajen gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC).
Kwamitin amintattun ya kuma bukaci NWC da ya gudanar da taron a watan Fabrairu 2025 kamar yadda aka shirya, tana mai gargadi cewa kara jinkiri zai tsananta matsalolin jam’iyyar.
Sanarwar bayan taron, ta jaddada muhimmancin hadin kai da bin dokokin jam’iyya, musamman wajen tabbatar da yankuna sun samu wakilci cikin kwamitin gudanarwa.n