Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar musulunci ta mayar da martani kan ficewar da wasu lauyoyi suka yi a matsayin bore kan ziyarar girmamawa da alkalan kotun suka kai wa wani basarake a Gaya.
A cewar mai magana da yawun kotun, Muzammil Ado Fagge, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ranar Juma’a, yace matakin lauyoyin ya samo asali ne daga rashin fahimtar al’adar kotun na kai ziyara ga shugabannin gargajiya masu daraja a duk inda ake gudanar da shari’a.
Ya bayyana cewa ziyarar alkalan zuwa fadar Sarki ba wai barin aikinsu ba ne, sai dai al’adar girmamawa.
Ya kara da cewa wannan al’ada ba sabuwa bace a Kano, domin alkalan kotu suna kai ziyara ga sarakunan gargajiya a wasu wuraren kamar Albasu, Ajingi, Kura da sauran yankuna wajen Kano
Idan za a iya tunawa cewa wata kafar labarai ta yanar gizo ranar Talata, 24 ga Disamba, 2024 ta bada rahoton cewa lauyoyi kimanin 15 sun yi bore tare da ficewa daga kotu, suna zargin cewa alkalan Kotun Daukaka Kara ta Shari’a a Kano, karkashin jagorancin Qadi Mukhtar Kunti, Qadi Mustafa Lalloki, da Qadi Aliyu Kani, sun bar aikinsu tare da saba lokacin zama na kotu don kai ziyara ga Sarkin Gaya.
Rahoton ya bayyana cewa, wani lauya da ke cikin kotun ya ce, “Alkalan sun zo harabar kotu kuma suka wuce ofishinsu bayan ƙarfe 11:00 na safe, maimakon ƙarfe 9:00 na safe kamar yadda sanarwar ta nuna tun ranar Litinin.”
“Sun makara awanni biyu sannan suka shiga ofishinsu. Duk lauyoyin da ke cikin kotun sun riga sun nuna rashin jin dadi amma mun kasance masu natsuwa tare da shirin cigaba da shari’ar. Duk lauyoyi sun riga sun sa hannu a jerin sunayen da kotu ta fitar.”
“Amma bayan da muka fahimci cewa alkalan sun bar harabar kotun ta wata ƙofa ta baya ba tare da sanarwa ba, duk lauyoyin sun yanke shawarar ficewa daga kotun ba tare da jiran dawowar alkalan ba,” in ji lauyan.
Sai dai a martanin da ya bayar, mai magana da yawun kotun, Muzammil Fagge ya jaddada cewa boren da lauyoyin suka yi ya saba dokokinsu, yana mai nuna bukatar fahimta da haɗin kai tsakanin lauyoyi da kotun Shari’ar Daukaka Kara.
Ya tabbatar da cewa kotun ba ta tsayar da zama ƙarfe 9:00 na safe ba, sabanin ikirarin lauyoyin.
Mai magana da yawun kotun ya nuna
Ya jaddada cewa ya kamata lauyoyi su kare darajar kotu da alkalan ta.