Naira miliyan 125 aka ware a kasafin kudin 2025, don kula da fulawa da dabbobin fadar Shugaban Ƙasa.
Wannan adadin ya haɗa da Naira miliyan 86 domin kulawa da dabbobi, da kuma Naira miliyan 38.5 na kula da ciyayi da fulawar fadar.
Wannan mataki na kulawa da dabbobi da shuke-shuke yana nuni da yadda Fadar Shugaban Ƙasa ke ba da muhimmanci wajen kula da kyawawan yanayin fadar da lafiyar dabbobi.
A cikin kasafin, an ware Naira miliyan 165 domin sayen tayoyi masu sulke,
Hakanan, an ware Naira biliyan 4.7 domin sayen sababbin motoci,
Kasafin na 2025 ya kuma ware Naira miliyan 101 domin sayen kayayyakin motsa jiki a Fadar Shugaban Ƙasa.
Har ila yau, an ware Naira miliyan 73 domin sayen na’urorin sadarwa, wanda zai tabbatar da ingantaccen sadarwa a tsakanin ofishin shugaban ƙasa da sauran sassan gwamnati.
A ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kudi na 2025 wanda ya kai Naira tiriliyan 49.
Tuni Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kansa, kuma a halin yanzu yana gaban kwamitin majalisar domin fara aiwatar da shi.