DOWNLOAD HERE

News

Kano: Gwamna Abba ya sallami SSG da kwamishinoni 5

DOWNLOAD HERE

Kano: Gwamna Abba ya sallami SSG da kwamishinoni 5
Written by Areatatafo

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, a wani sabon tsarin sauya mukamai, ya kori Sakataren Gwamnati (SSG), Abdullahi Bichi, da Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Shehu Sagagi, sannan ya sauya wurin aikin Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawkin Tofa, ya bayyana cewa an sallami SSG Bichi ne saboda matsalar lafiya, yayin da ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan aka rusa gaba daya.

Make money online

Gwamna Yusuf ya kuma sallami kwamishinoni biyar.

Wadanda aka kora sun hada da Ibrahim Jibril Fagge, na ma’aikatar kudi; Ladidi Ibrahim Garko ta ma’aikatar al’adu da wawon bude ido; Baba Halilu Dantiye na ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin cikin gida; Shehu Aliyu Yammedi na m’aikatar qyyuka na musamman; da Abbas Sani Abbas, na ma’aikatar raya karkara da ci gaban al’umma.

Gwamnan ya umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da kwamishinonin biyar da aka sallama da su garzaya ofishin gwamna don yiwuwar sake ba su sabbin mukamai.


Leave a Comment

//leeteehigloothu.net/4/7617614