Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kano ta sanar da ranar 1 ga watan Junairu, 2025 a matsayin ranar rufe tattara kudaden ajiyar maniyyata a jihar.
Kakakin hukumar Suleman Dederi, ya ce babban daraktan hukumar Lamin Rabi’u Danbappa ne ya sanar da hakan a yayin taron jami’an hukumar alhazai na kananan hukumomi, wanda ya gudana a yau a ofishin sa.
Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya jaddada cewa wa’adin ya yi daidai da jadawalin aikin Hajji na 2025 da Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta fitar, wanda ya wajabta wa dukkan jihohin kasar su mika bayanan maniyyatan su ga hukumar a ranar 7 ko kafin ranar 7 ga watan Janairun 2025 don tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
Babban Daraktan ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun karancin sayar da kujerun aikin Hajji a halin yanzu, ya kuma bukaci jami’an hukumar na kananan hukumomi da su kara zage damtse wajen sayar da kujerun da aka ware musu.
Ya yi kira da a samar da sabbin dabaru don bunkasa sayar da kujerun a cikin wa’adin da aka kayyade.