Wani hatsarin mota da ya afku da safiyar Laraba ya jikkata mutane 22 yayin da mabiya addinin Kirista ke gudanar da tattakin bikin Kirsimeti a cikin birnin Gombe, kamar yadda suka saba yi a kowace shekara.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Buhari Abdullahi, ya ce wata mota ƙirar Sharon da aka loda da kayan hatsi ta afka cikin masu tattakin daga baya, inda ta buge mutane da dama.
“Wasu daga cikin wadanda suka ji rauni sun samu karaya, kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawa,” in ji ASP Abdullahi.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun ceci direban motar daga hannun wasu mutane da suka yi kokarin kai masa hari cikin bacin rai.
Bikin Kirsimeti ya gudana cikin kwanciyar hankali a mafi yawan sassan Najeriya, ba tare da wata matsalar tsaro ba.