Wata gobara ta yi sanadiyyar rasuwar wani magidanci mai shekara 67, Muhammad Uba, da matarsa mai shekara 52, Fatima Muhammad a Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Jumma’a a unguwar Rangaza Layin AU da ke karamar hukumar Ungogo.
A cewar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, dakin kula da ayyukan gaggawa na hukumar ya karɓi kiran neman agaji daga ɗaya daga cikin ma’aikatansa, FS Ahmad Abubakar, da misalin ƙarfe 01:45 na safe.
Ya ce, “Ma’aikatan da ke bakin aiki a tashar kashe gobara ta Bompai sun tafi wurin da abin ya faru kuma sun isa wurin da misalin ƙarfe 01:51 na safe. Lokacin da suka isa, sun tarar gobarar ta riga ta yi sauƙi.
“Wuta ta kama ɗakuna biyu kuma sun ƙone sosai. A halin da ake ciki, wani mutum mai shekara 67 mai suna Muhammad Uba da matarsa mai shekara 52, Fatima Muhammad, sun makale a cikin hayaki. An ceto su a sume tare da rauni a wasu sassan jikinsu, amma daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsu.”
Abdullahi ya ƙara da cewa, an miƙa gawawwakin ga shugaban unguwar Rangaza, Muhammad Auwalu Rayyanu, a karamar hukumar Ungogo, yayin da ake ci gaba da binciken sanadiyyar tashin gobarar.