DOWNLOAD HERE

News Politics

Danagundi ya taya Ganduje murnar cikarsa shekaru 75

DOWNLOAD HERE

Danagundi ya taya Ganduje murnar cikarsa shekaru 75
Written by Areatatafo

Shugaban Cibiyar Kula da Ingancin Ayyuka ta Kasa, Dr. Baffa Babba Dan-agundi, ya taya Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 75, inda ya bayyana shi a matsayin “Mafi Nasara na Dukan Lokuta.”

Dan-agundi a cikin sakon murnar ranar haihuwa na musamman da ya aike wa tsohon gwamnan Jihar Kano, a ranar Laraba, ya ce shugabancin Ganduje na hangen nesa ya kawo gagarumin ci gaba ga Jihar Kano da Jam’iyyar APC.

Make money online

“Ka lashe Jihohin Kogi, Edo, da Ekiti a ƙarƙashin jagorancinka, rikicin cikin APC ya ragu, kuma ka gina ƙauna ga ƙasar a cikin zukatan wakilanmu da aka zaba.

“Baba, ina maka fatan zaman lafiya mai ɗorewa da lafiyar jiki domin jagorantar jam’iyyarmu zuwa nasara a Zaben 2027.”


Leave a Comment

//psoahegauku.net/4/7617614