DOWNLOAD HERE

News

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta MNJTF sun hallaka yan Boko Haram 10

DOWNLOAD HERE

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta MNJTF sun hallaka yan Boko Haram 10
Written by Areatatafo

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta MNJTF sun yi nasarar dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a sansanin soji da ke Darak a kasar Kamaru, inda suka kashe ‘yan ta’adda 10.

Sanarwar da babban jami’in yada labaran soji na MNJTF, Lt.-Col. Olaniyi Osoba ya fitar, ta bayyana cewa, an kai musu harin ne da sanyin safiyar ranar 18 ga watan Disamba, 2024, inda ‘yan ta’addan suka kai farmaki daga wurare da dama a sansanin sojojin na Darak.

Make money online

Sai dai ya ce, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda suka harbe ‘yan ta’adda shida nan take tare da tilasta wa sauran guduwa da raunuka daban-daban na harbin bindiga.

Lt.-Kol. Osoba ya bayyana cewa, wasu sojoji biyar sun samu raunuka a yayin artabun wanda a halin yanzu ke samun kulawa a asibiti.

Sanarwar ta kara da cewa, a wani samame na bin baya da sojojin suka kai wa ‘yan ta’addan da suka tsere, a kauyen Mazogo da ke tsakanin Zamba da Djibirilli, an yi nasarar harbe hudu daga cikinsu tare da kwato kayayakin abinci na ‘yan ta’addan.


Leave a Comment

//tituwhahooghe.net/4/7617614