DOWNLOAD HERE

News

An rabawa manoman alkama 6000 tallafi a Kano

DOWNLOAD HERE

An rabawa manoman alkama 6000 tallafi a Kano
Written by Areatatafo

Ministan Noma da, Abubakar Kyari, ya kaddamar da rabon kayan tallafi ga manoman alkama 6,000 a jihar Kano

Ministan, wanda ya samu wakilcin Ko’odinetan Kano na shirin bada tallafin a Ma’aikatar Noma Isa Hotoro, ya bayyana hakan a cibiyar tattara amfani da ke Alkamawa, karamar hukumar Bunkure.

Make money online

Ya ce rabon kayan tallafin, wanda ke karkashin shirin musamman na Gwamnatin tarayya kan noman alkama, ana sa ran zai karfafa noman alkama, duba da cewa gwamnati ta bayar da tallafi da kaso 75 cikin 100 na farashin kayan.

“Duk wani manomi zai karɓi buhu uku na taki da buhu ɗaya na irin alkama mai nauyin kilogiram 50 a kan farashin N111,000, wanda ke wakiltar kaso 25 cikin 100 na jimillar farashin kayan,” ya kara da cewa.

A cewarsa, ana sa ran manoman za su noma gonaki masu fadin hekta 3,000 a cikin kungiyoyin noma guda 12 da ke Alkamawa a Bunkure, Ajingi da kuma Gaya.

“Duk wani manomi ana sa ran zai noma hekta rabin hekta a cikin wadannan kungiyoyi noma na musamman guda 12 da ke Alkamawa, Ajingi da Gaya,” ya bayyana.

A wata tattaunawa wasu daga cikin manoman sun nuna godiyarsu ga Gwamnatin Tarayya bisa wannan tallafi, duba da cewa tsadar kayan aiki da sufuri ya tilasta wa mafi yawan manoma rage adadin gonakin da suke nomawa.

Sai dai sun roki gwamnati da ta tabbatar da rabon kayan tallafin cikin lokaci domin ba manoma damar fara shirye-shiryen noma tun da wuri.


Leave a Comment

//grudaiwoomsoa.net/4/7617614