DOWNLOAD HERE

News

An kama yan tawayen Kamaru a Najeriya

DOWNLOAD HERE

An kama yan tawayen Kamaru a Najeriya
Written by Areatatafo

Sojojin rundunar ta 6, sun kama mutane hudu da ake zargi da zama mambobin ‘yan tawayen Ambazonian a Taraba.

Ambazonia ƙungiya ce ta ‘yan tawayen da ke aiki a ƙasar makwabciyar kasa Jamhuriyar Kamaru.

Make money online

A cikin wata sanarwa da Capt. Olubodunde Oni, ya fitar ranar Asabar a Jalingo daga Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Sojojin Nijeriya, ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a wani otel a garin Takum.

Sanarwar ta ce, bisa ga sahihin bayanan sirri da aka samu, an bi sawun masu laifin har lokacin da aka kama su. Kuma tuni suka amsa cewa suna daga cikin ƙungiyar ‘yan tawayen da ke kai hari da yaki da amfani da bindigogi tare da haɗin gwiwar wasu ‘yan Nijeriya.

Sanarwar ta kara da cewa an kwato wayoyi guda hudu daga hannun wadanda ake zargin, wadanda yanzu haka suna tsare yayin da ake cigaba da bincike.

Haka kuma, a cikin wani aiki na daban, bisa ga bayanan sirri da aka samu, sojojin da aka tura zuwa Natilde a yankin Bantaji na karamar hukumar Wukari sun kama wata mota wadda ke dauke da bututun mai guda 19 da aka sata wanda ke naɗe da tambarin Kamfanin Mai na kasa (NNPCL).

Sanarwar ta bayyana cewa, ci gaba da haɗin gwiwa tare da Hukumar Tsaro ta Ƙasa (NSCDC) a sashen Wukari ya kai ga samun ƙarin bututun 11, wanda ya haifar da jimillar bututun 30 da aka samu.

“An mika kayan da aka kwato ga NSCDC na sashen Wukari don ci gaba da bincike da kuma daukar matakin da ya kamata.


Leave a Comment

//shutheeckauftog.net/4/7617614