Gwamnatin Kano za ta dauki sabbin ma’aikatan lafiya a fadin jihar domin inganta bangaren.
Darakta mai kula da harkokin lafiya a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano Hajiya Aisha Abdulqadir Makkatu ce ta bayyana hakan a ranar Talata.
Ta kuma ce hukumar ta su na gudanar da wasu ayyuka kyauta da su ka hadar da gwajin sukari, hawan jini da bayar da magunguna.
Ta kuma ce tuni aka samar da kwamiti na musamman wanda al’umma za su dinga kai kokensu a kowanne karamin asibitin jihar.