DOWNLOAD HERE

News

Sama da jihohi 10 na amfana da kogin Watari

DOWNLOAD HERE

Sama da jihohi 10 na amfana da kogin Watari
Written by Areatatafo

Manoma daga jihohi goma ne ke amfana da gyaran tafkin Watari da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Anyi gyaran tafki ne da haɗin gwiwar shirin sauya fasalin noma na tarayya (ATAP).

Make money online

Manajan aikin, Malam Mohammed Tijjani-Kwa, ya bayyana cewa manoman da ke cin gajiyar aikin sun haɗa da waɗanda ke Jihar Kano da makwabtan jihohi irin su Katsina, Jigawa, da Kaduna.

Tijjani-Kwa ya ce manoman daga waɗannan jihohi suna yin haya wajen samun filayen noma daga abokan aikinsu na Bagwai domin noma.

Ya ƙara da cewa, “Su tare da abokan aikinsu na Bagwai suna shuka irin kayan amfanin gona kamar albasa, dawa, letus, shinkafa da kokwamba, waɗanda suke samun ruwa daga tafkin da ake gyarawa.”

Da yake yi wa manema labarai bayani a yayin zagayawa da su a wajen aikin tafkin wanda ya kai naira biliyoyin, Manajan ya ce tafkin zai iya bayar da ruwa don noman kadada 917 na gona.

Tijjani-Kwa ya ce, kusan manoma 25,000 ne ke amfana daga tafkin, kuma ayyukan da suke yi a wajen sun canza rayuwarsu.


Leave a Comment

//goazooviwhail.net/4/7617614