Hukumar Inshorar bankuna ta kasa (NDIC) tace zata fara biyan wadanda suka ajiye kudin da ya haura Miliyan 5 a bankin Heritage da ya durkushe kwanan baya.
Babban Daraktan hukumar Mista Bello Hassan ne ya bayyana haka a wajen bikin ranar NDIC ta musamman a bikin baje kolin kasuwanci da ake gudanarwa a Kano.
Hassan ya ce, “hukumar NDIC ta taka rawar gani wajen tabbatar da cewa lokacin da bankuna suka gaza, ana kare hakkokin masu ajiya, a kuma dawo da kudaden su cikin gaggawa”
“Tun bayan soke lasisin aiki na bankin Heritage a ranar 3 ga watan Yuni, 2024, an fara biyan wadanda sukayi ajiya kasa da Naira miliyan 5, ta hanyar amfani da Lambobin BVN don gano masu ajiya a wasu bankunan ba tare da buƙatar cike fom ko ziyartar ofisoshin NDIC ba. Yanzu, mun himmatu wajen ganin an biya masu ajiyar kudin da ya haura Naira miliyan 5 hakokinsu.” a cewarsa.