DOWNLOAD HERE

News

70% na tsaron kasa ya dogara ga siyasa – Janar Christopher Musa

DOWNLOAD HERE

70% na tsaron kasa ya dogara ga siyasa – Janar Christopher Musa
Written by Areatatafo

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce akalla 70% na tsaron kasa ya dogara ne ga siyasa da walwalar tattalin arziki.

Ya ce karfin soji kawai ba shi ne ne samar da tsaron da Najeriya ke bukata ba a halin rashin tsaro da ake fuskanta.

Make money online

Ya ce amfani da karfin soji na bayar da gudummawar 30% na tabbatar da tsaro.

Janar Musa ya bayyana haka ne a wani taro kan tsaron ƙasa da cibiyar dakile ayyukan ta’addanci karkashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro ya shirya a Abuja.

Babban hafsan ya ce su kadai ba za su iya maganin matsalar rashin tsaro a Najeriya ba.

“Dole ne a hada karfi da karfe wajen magance matsalar tsaro, musamman ganin rikice-rikice da kuma rashin tabbas da ya dabaibaye mutane,” in ji shi.

Janar Christopher Musa ya kara da cewa mutanen gari da yan jarida na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen wanzuwar zaman lafiya.


Leave a Comment

//taucounaglie.net/4/7617614